Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Kano na kokarin gogayya da kasashen da suka cigaba kan harkokin kudi

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi rahoton kwamitin wucin gadi kan dokar harkokin kudi ta shekarar 2019 wanda majalisar ta kafa don ya rika bibiyar yadda ake ta’ammali da kudade a ma’aikatun gwamnati.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya gabatar da rahoton a zaman majalisar na yau Talata.

Bayan fara zaman majalisar ne kakakin majalisar Abdul’aziz Garba Gafasa ya baiwa shugaban kwamitin damar fara gabatar da rahoton.

Labarai masu alaka:

Majalisar Kano ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar

Abdul’aziz Garba Gafasa ya sake zama shugaban majalisar dokokin jihar Kano

Da yake tattaunawa da manema labarai bayan kammala gabatar da rahoton, mataimakin shugaban majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya ce, kafa dokar na da matukar muhimmanci la’akari da irin tanadin da aka yi wajen kafa ta.

Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano.

Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya rawaito cewa mataimakin kakakin majalisar ya kuma bayyana cewa, an kirkiri dokar ne da nufin zamanantar da ayyukan gwamnati a jihar Kano, ta yadda za ta yi dai-dai da yadda ake gudanar da ayyuka a kasashen da suka cigaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!