Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna bukatar kamfanin da zai gyara matatar mai ta fatakwal ya kammala cikin watanni 8 – NNPC

Published

on

Kamfanin samar da man fetur na kasa NNPC ya sanya hannu da wani kamfanin da zai aikin gyara matatar mai ta garin Fatakwal bisa yarjejeniyar kammalawa cikin watanni goma sha takwas.

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala sa hannun kan yarjejeniya tsakanin kamfanonin biyu a Abuja.

Mele Kyari yace aikin gyara matatar man zai lakume kudi kimanin dala amurka biliyan daya da rabi.

Ya kara da cewa cikin watan jiya ne majalisar zartarwa ta amince da biyan kudin farfado da matatar man da yakai dalar amurka biliyan daya da rabi wanda ake sa ran kammala aikin cikin watanni goma sha takwas wanda zai sa ta fara samar da mai kaso 95 cikin dari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!