Labarai
Muna bukatar mata a rundunar mu: Civil Defence
Rundunar tsaro ta Civil Defense a Jihar Kano tayi kira ga mata ‘yan asalin jihar Kano dasu rika shiga rundunar ana gudanar da aiki dasu sakamakon yadda rundunar take fuskantar matsalar karancin ma’aikata mata don gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Kwamanadan rundunar na Kano Muhammad Lawan Falala ne ya bayyana hakan lokacin daya kaddamarda wata runduna ta musamman ta mata zalla da zasu rika samarda tsaro a makarantun kwana da sauran gurare mallakar gwamnati jihar.
A cewarsa suna fuskantar karancin ma’aikata mata a rundunar a Kano, domin ko abaya – bayan nan ma mace daya ce ‘yar asalin jihar Kano ta nemi aiki da rundunar.
Muhammad Falala ya Kara da cewa ‘saboda karancin matan da suke fuskanta a rundunar a yanzu haka yasa dole sai sun rubutawa shalkwatar rundunar bukatar neman karin ma’aikata mata saboda makarantu a jihar Kano suna da yawa.
Freedom Radio ta rawaito cewa kwamandan rundunar na kira ga iyaye dasu rika barin ‘ya’yansu mata suna shiga rundunar ba sai dole sun mika bukatarsu ga shalkwatar rundunar ta kasa ba.
RAhoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login