Labarai
Muna ci gaba da tattara bayanai bisa zargin badakalar da ake yi waGanduje- PCCPC

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci a Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da zurfafa bincike kan badakalar da ake zargin tsohon Gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban Hukumar, Alhaji Sa’idu Yahaya, ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawar sa da Freedom Radio yau Litinin.
Alhaji Sa’idu Yahaya, ya kuma bayyana cewa hukumar na ci gaba da tattara muhimman bayanai da suka shafi zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan na Kano.
You must be logged in to post a comment Login