ilimi
Muna ci gaba da tattaunawa da wakilan Gwamnatin Tarayya- ASUU

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU, ta tabbatar da cewa ta na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya da Alhaji Yayale Ahmed ke jagoranta, yayin da yajin aikin gargadin na mako biyu da ASUU din ke yi yanzu haka ya shiga rana ta bakwai.
Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa Farfesa Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa, an samu ci gaba a bangarori biyar daga cikin bukatun su guda bakwai da suka hada da biyan hakkokin su da suke bin gwamnati ba shi.
Ya kuma bayyana cewa, an samu shiga tsakani daga wasu fitattun ’yan kasa don kawo karshen rikicin. ASUU ta bukaci mambobinta da su ci gaba da kasancewa masu juriya da hadin kai, tare da bin umarnin shugabannin rassan su. Yajin aikin dai yana da nufin matsa wa gwamnati lamba kan aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla dan inganta walwalar malamai da harkar ilimi.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin din da ta gabata 13 ga wannan wata. Kungiyar ta Asuu ta nasar da tsunduma yajin aiki gargadi na makwanni 2.
You must be logged in to post a comment Login