ilimi
Muna da ƙarancin kayan koyo da koyarwa a makarantu – NUT
Kungiyar malamai ta kasa rashen jihar Kano NUT ta bayyana cewa baban Ƙalubalen da suke fuskanta bai wuce na rashin kayan koyo da koyarwa.
Kazalika ƙungiyar ta kuma ce, akwai cunkoso a azuzuwan makarantu musamman ma a jihar Kano.
Shugaban kungiyar Muhammad Abubakar ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar malamai ta duniya.
Ya ce “Tun bayyan da gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ilimi kyauta kuma dole ga ɗaliban Kano, ana fuskantar yawan ɗalibai da kuma rashin isassun kayan koyo da koyarwa a makarantu”.
Kungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta da bai wa malamai a makarantu horo na musamman, kasancewar da dama daga cikin malaman ba su da ƙwarewar koyarwa.
Taken bikin ranar malamai ta duniya a bana shi ne Malamai ke da haƙƙin kawo gyara a harkokin ilimi.
You must be logged in to post a comment Login