Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

RAHOTO : Yadda bikin ranar Malamai ta Duniya ya gudana

Published

on

Daga Maryam Ali Abdallah

Hukumar raya ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO ta ware ranar 5 ga watan oktobar ko wace shekara ta zama ranar malamai ta duniya a shekarar 1994.

Ranar na mayar da hanakali ne wajen nuna muhimmancin da malamai ke da shi da kuma rawar da suke takawa don inganta rayuwar al’umma.

UNESCO ta kaddamar da ranar malamai ta duniya a shekarar 1994 don mayar da hankali kan gudunmawar malamai suka bayar da kuma nasarorin da malaman suka samu da kuma nuna damuwa kan halin da suke ciki.

Haka zalika ranar na karrama malamai bisa fifikon da suke da shi a tsakanin al’umma don kara zaburar da su.

To ko ya ya malamai su ke a wannan lokaci? Wasu da muka zanta da su sun bayyana cewa “ Kalubalen bai wuce yadda ake zaftare musu albashin su a kowanne wat aba, da kuma rashin yi musu karin girma akan lokaci baya ga rashin kayan aiki a makarantun”.

A nasu bangaren wasu tsofaffin shugabannin wasu makarantu a nan Kano, sun yi bayani game da halin da malamai ke tsintar kan su a ciki, inda suka ce “ ga dukkanin malamin da yayi ritaya daga aiki to babbar matsalar bata wuce rashin fitowar kudadenua na sallama daga aiki a kan lokaci ba”.

A na sa bangaren shugaban kungiyar malamai ta kasa NUT reshen jihar Kano Malam Hambali Muhammad, ya bayyana irin kalubalen da suke fuskanta inda ya ce, “hikimar dake cikin kebe ranar bai wuce duba irin matsalolin da malamai ke ciki ba, tare da magance musu ita”.

Ya kara da cewa “yi wa malamai karin girma a lokacin da ya dace tare da samar musu isassun kayan koyarwa da kuma biyansu hakkokinsu yadda ya kamata a kan lokaci, zai taimakwa wajen kara bunkasa harkokin ilimi a kasar nan”.

Taken bikin na bana shi ne: jagoranci a cikin rikici, don sake tunanin makoma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!