Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna da kwararan hujjoji Atiku ne ya samu nasara a zaben 2019 – Bala Muhammed

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, ya ce, suna da kwararan hujjoji da suka nuna cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar shine wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2019.

A cewar Bala Muhammed shugaba Buhari ya sha kaye a zaben da ya gabata a 2019, kawai dai wasu hanyoyi aka bi aka yi magudi da ya bai wa jam’iyyar PDP rashin nasara.

Gwamnan na Bauchi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels (POLITICS TODAY) a daren jiya alhamis.

‘‘Muna da hujjoji da suka nuna akwai fahimtar juna tsakanin hukumar zabe da jami’an tsaro wanda shine ya sanya jam’iyyar PDP ta yi rashin nasara’’.

‘‘Na tabbata ‘yan Najeriya suna sane da halin da aka shiga lokacin zaben da kuma irin abubuwan da suka faru, sai dai jam’iyyar PDP a yanzu ta koyi darasi’’

‘‘Ba za mu sake yadda mu zura ido ayi mana abin da ya faru a baya ba, za mu yi gyara tare da tabbatar da mun toshe duk hanyoyin da aka bi aka yi mana magudi a zaben da ya gabata’’. Inji Bala Muhammed.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!