Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojin Najeriya sun samu nasarar kashe yan ta’adda a zamfara

Published

on

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na ‘Operation Hadarin Daji’ sun yi nasarar dakile ayyukan ‘yan ta’adda, tare da kashe wasu da dama a kauyen Kabasa da ke karamar hukumar Magami a Zamfara.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Birgediya janar Mohammed Yerima, ne ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitara a Juma’ar nan.

Yerima ya ce, sojojin sashi na 3 sun afka wa kauyen ne bayan wani bayanin sirri da suka samu game da harin da ‘yan ta’addan ke shirin kai wa mazauna yankin.

Ya ce isowar sojojin cikin lokaci ya dakile mummunan nufin ‘yan ta’addar da ke shirin kai wa.

Yerima ya kara da cewa, cikin hanzari sojoji suka yi nasarar cafke ‘yan ta’addar inda suka samu nasarar kashe wasu da yawa yayin da wasu suka tsere zuwa daji da raunukan harsasai.

A cewarsa, soja daya ya rasu yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban a yayin arangamar kuma suna karbar magani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!