ilimi
Muna gab da kammala Sauya tsarin Manhajar karatun Sakandare- Ministan Ilimi
Gwamnatin tarayya ta ce tana gab da kammala Sauya tsarin Manhajar Karatun Makarantun Sakandare.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a taron ƙasa da ƙasa na ƙungiyar masu tsara manhajar ilimi ta Afirka, wanda aka gudanar a Abuja.
Ya kuma ce tuni an kammala kuma an amince da sabuwar manhajar karatun firamare da kuma sakandare na ƙasa (daga aji ɗaya zuwa na uku). Sai ya ce yanzu ana kan matakin ƙarshe na sauya manhajar matakin makarantun sakandare.
Ministan, wanda mataimakiyar sa, Farfesa Suwaiba Ahmad ta wakilta, ya tabbatar da cewa sabon tsarin makarantun sakandare da ake shirin ƙaddamarwa zai yi daidai da ƙa’idojin ilimi na duniya.

You must be logged in to post a comment Login