Labarai
Muna iya kokarin mu wajen shawo kan matsalar rashin tsaro – Shugaban Kasa Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa batun tsaro shi ne babban ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu, musamman a yankin Arewa.
Tinubu, wanda ya yi jawabi a Kaduna ta bakin Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a wajen taron cika shekaru 25 da kafa Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ya ce gwamnati na ƙoƙari sosai wajen shawo kan ayyukan ’yan bindiga da sauran masu tayar da hankali waɗanda ke da cikas ga ilimi da ci gaban tattalin arziƙin kasar.
Ya kuma bayyana cewa abubuwan da suka fi damunsa sun fi karkata ne kan matsalolin tsaro da ke addabar Arewacin ƙasar, yana mai cewa ba za a samu ci gaban da ake buri ba muddin wani yanki na ƙasa na cikin mawuyacin hali.
Haka kuma, ya jinjinawa ACF bisa rawar da take takawa wajen haɗa kai a Arewa.
You must be logged in to post a comment Login