Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kawo ƙarshen faɗan daba a kano-Gwamna Abba

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yayi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kawo ƙarshen faɗan daba a faɗin jihar, da kuma kira ga alƙalai dasu kasance masu zartar da hukunci ga duk wanda aka kama da tayar da hankali al’umma domin ya zama darasi ga ƴan baya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi wannan jawabin ne da safiyar yau yayin taron majalisar zartarwa da gwamnati take yi a duk sati domin aiwatar da aikace-aikacen gwamnati.

Gwamna Yusuf kuma yi kira ga alƙalai da su zartar da tsatstsauran hukunci akan duk wanda aka samu da laifin faɗan daba.

Gwamna Yusuf ya kuma umarci dukkannin shugabannin ruƙo na ƙananan hukumomi 44 da su shiga lunguna da saƙo na jihar nan domin samar da ruwa musamman rijiyoyin birtsate.

Haka kuma gwamnatin jihar Kano ta ce zatayi dukkannin mai yihuwa wajen kawo ƙarshen faɗace faɗacen daba a faɗin kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!