Labarai
Muna neman goyon bayan Obasanjo a zaben 2027- PDP

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Kabiru Taminu Turaki ya bayyana cewa sun kai wa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ziyara ne domin neman shawarwari da goyon baya gabanin zaben 2027.
Turaki, wanda ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa a kwanakin baya, ya ziyarci Obasanjo a garin Abeokuta, da ke Jihar Ogun, tare da wasu manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugaban kwamitin Amintattu na jam’iyyar, Sanata Adolphus Wabara, da wasu tsofaffin gwamnoni.
Ya ce ziyarar wani bangare ne na gabatar da sabon shugabancin jam’iyyar ga tsohon shugaban kasar.
You must be logged in to post a comment Login