Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna neman matashin da ya yi ikirarin daina yin Sallah ruwa a jallo – Ibn Sina

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce, tana neman matashin nan ruwa a jallo da yayi ikirarin daina yin sallah sakamakon yi masa aski da aka yi.

Babban kwamandan Hisbah Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan, a wani sakon murya da ya aikewa Freedom Radio.

Tun da fari dai wani faifan bidiyon ne ya karade shafukan sada zumunta da ke bayyana matashin na bayanin cewa ya daina Sallah tunda har aka aske masa sumar da ya dade yana tarawa a kan sa.

“Wannan ne ya janyo hankalin mu a hukumar Hisbah kasancewar ana ta yada cewa a hukumar aka yi masa askin tare da bulala talatin, a don haka muke nesanta kan mu daga wannan zargi” inji Ibn Sina.

Ibn Sina ya jaddada cewa hukumar na neman tatashin Ruwa a Jallo
sakamakon munanan lafazin da ya yi da rashin ladabi ga shari’ar Musulinci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!