Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba za mu lamunci kazanta a ma’aikatun gwamnati ba – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta aikewa da hukumar KAROTA takardar gargadi sakamakon rashin tsaftar bandakunan su.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Getso ne ya bada umarnin, wanda Babban sakataren ma’aikatar muhalli Adamu Abdu Faragai ya wakilce shi.

Umarnin ya biyo bayan duban tsaftar muhalli na karshen wata da ma’aikatar muhalli ta kai hukumar ta KAROTA.

Adamu Abdu Faragai ya umarci kwamitin da ke lura da tsaftar muhalli cewa ya aikewa hukumar KAROTA takardar gargadi tare da kwalejin harkokin lafiya da kimiyya sakamakon rashin tsaftar bandakunan su.

Sai dai ma’aikatar muhallin ta yabawa sakatariyar karamar hukumar Nasarawa bisa tsaftar muhalli da suka yi har ma ta basu lambar yabo.

A juma’ar karshen kowanne wata ne ake gudanar da duban tsaftar muhalli a ma’aikatun gwamnati da tashoshin mota har ma da kasuwanni.

Sai dai a karo na biyu kenan tawagar tsaftar muhalli na kai ziyara hukumar KAROTA ba tare da samun tarba daga shugabannin ta ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!