Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna roko gwamnati Kano ta kara wa’adin tarewarmu a Kasuwar magani ta kasuwar Dan Gauro: Masu Magani

Published

on

 

Kungiyar masu sayar da magunguna ta jihar Kano, ta bukaci gwamnati data kara musu wa’adin data dibar musu kafin komawar su, kasuwar Dan Gauro.

Salisu Tijjani Datti mamba a kungiyar ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakiliyar mu Zahra’u Sani Abdullahi a safiyar yau.

Salisu Tijjani Datti ya kuma kara da cewar suna bukatar a wadata su da shago tare da samar da tsaro a wajan ta yadda zasu samu damar gudanar da kasuwancin su cikin kwanciyar hankali.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/HANTSI-KUNGIYA-27-01-2023.mp3?_=1

Salisu Tijjani Datti, ya kuma ce kungiyar za ta fito da sababbun hanyoyin da za su magance matsalar sayar da magungunan da wa’adin amfani dashu ya kare.

Tun bayan da gwamnatin Kano ta umarci masu sayar da magani a kasuwar sabon gari, dama sauran kasuwanni dasu tashi su koma kasuwar da aka ware musu.

sai dai da yawan daga cikin ‘yan kasuwar na ganin cewar an yi hanzarin tilasta musu tarewa a kasuwar don kuwa akwai ayyukan da ba a kammala ba a saboda haka suke rokon a dage tarewar tasu.

Rahoton:Zara’u Sani Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!