Labarai
Muna samun nasara kan ‘yan ta’adda – Sojin Najeriya

Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da samun nasara a ci gaba da kai farmaki da take yi kan yan ta’adda a sassan kasar nan
A cikin wata sanarwa da Shelkwatar sojin Kasa ta fitar a shafinta na Facebook a daren jiya Talata ta ce cikin awanni 72 da suka gabata dakarunta sun kashe kusan yan ta’addan 47 a hare hare daban daban a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.
Haka zalika sun ce an Kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka sannan an ceto sama da mutane 30 da aka sace a yayin sumamen.
Sojojin sun kwato tarin makamai da harsasai da kayan aiki bayan gudanar da hadin gwiwar hare haren Kasa da na sama bisa samun bayanan sirri.
You must be logged in to post a comment Login