Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Operation Accord ta kashe ‘yan tada kayar baya a Kaduna

Published

on

Rundunar sojin kasar nan na Operation Accord sun kashe ‘yan tada kayar baya hudu a jihar Kaduna tare da gano wasu muggan makamai ciki har da alburusai.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta kasa Manjo Janar John Eneche ne ya bayyana hakan, biyo bayan ci gaba da samun hare-haren ‘yan tada kayar bayan a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce rundunar sojin tayi wannan nasara ne a biyu ga watan da muke ciki na Satumbar bana.

Ya kara da cewa jami’an rundunar sun bude musu wuta ne bayan da suka arba da su, inda suka kashe mutum hudu bayan sauran da suka tsere sun samu raunuka a jikin su.

Yayin harin jami’an sojin sun samu bindiga kirar AK 47 daya da sauran bindigogi daban-dabam.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!