Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun samar da hanyoyin ratse domin gudanar da aikin gadar ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi dake ƙaramar hukumar Birni domin samarwa da al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce gwamnatin Kano zata sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci shiyasa yanzu haka gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Haka kuma gwamnan ya ce an samar da hanyoyin da al’umma zasu bi domin samin saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin.

Haka kuma gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanin lokaci domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!