Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta kawo mana dauki – Al’ummar Faggen-Kankara

Published

on

Al’umman dake unguwar Fegen-kankara mazabar yarimawa a karamar hukumar Tofa sun yi kira da dabbar Murya ga gwamnatin jahar Kano da ta duba halin da mutanen yanki suke ciki na lalacewar da hanyar su tayi wacce har sai da kai ga karyewar Gadar Watari.

A lokacin da yake jawabinsa ga menema labarai dagacin Garin Yarimawa Yahaya Mahammad na ta’ala ya bayyana cewa tsawun lokaci suka dauka suna kiraye-kiraye ga gwamnati da ta duba halin da  hanyar take ciki tun kafin takai ga karyewar gadar

Yahaya Mahammad Na ta’ala ya bayyana wa wakilin mu Umar Lawan Tofa cewa, matukar gwamnatin bata gyara hanyar ba toh babu shakka garuruwa sama da bakwa ne zasu shiga wani hali musamman ma a wannan lokacin na damuna.

Mahammad Na ta’ala ya ce halin da gadar ke ciki a halin yanzu mussaman ma idan an koma makarantu yara ba za su sami damar zuwa makaranta ba, kasancewar babu kyakyawar hanya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,158 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!