Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Al’umma su duba sabon jinjirin watan Zulhajji – Sarkin musulmi

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bukaci alummar musulami da su duba sabon watan Zulhajji na shekarar nan da muke ciki na 1441 daga gobe Talata bayan da watan Zulki’ida ya cika kwanaki 29.

Alhaji Muhammad Sa’ad na III ya ce sabon watan na Zulhijja shi ne nuna ranar da za’a sallah babba da kuma ranar tsayuwar Arafat.

Shugaban kwamitin bada shawarwari da al’amuran addini farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanar da hakan a yau Litinin yana mai yin kira ga alummar musulmai da su daba sabon jinjirin watan na Zulhijja.

Shugabannin KUST Wudil sun kai wa Sarkin Kano ziyara

Sarkin musulmi ya bukaci gwamnatin tarayya ta zage dantse don magance matsalolin tsaro

Jam’iyyar APC ta karyata rade-radin cewa tana shirye-shirye tsige mai alfarma sarkin musulmi

Akan haka ne Sarkin musulmin ta cikin sanarwar ya bukaci al’umma tun daga gobe Talata su duba watan don kai rahoto ga masu unguwanni na kusa da su kasancewar wata ne mai alfarma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!