Labarai
Muna tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro a Mali – ECOWAS
Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS sun ce za su ci gaba da tattaunawa kan matakan dakile tashe-tashe hankula da ke tunkarar kasar Mali a Litinin din makon gobe.
Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Juma’a.
Rahotanni na nuni da cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Bamako na kasar Mali a wani mataki na tattaunawa da takwarorinsa da ke kokarin shawo kan matsalar rashin zaman lafiya da ake fuskanta a kasar ta Mali.
Adesina ta cikin sanarwar da ya fitar na cewa, zaman shugabannin na ranar Litinin na da matukar muhimmancin gaske, saboda za su fito da matakai da za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin da suka ki-ci suka ki-cinyewa.
Cikin sanarwar dai, shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS kuma shugaban kasar Niger Muhammadou Issoufou na cewa, hadakar shugabannin za suyi dukkan mai yiwuwa wajen sanya matakan da za su kawo zaman lafiya a daukacin kasar ta Mali.
You must be logged in to post a comment Login