Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muna zama da yunwa sakamakon rashin kudi- Rahoto na musamman

Published

on

Al’umma na cewa, duk da kara wa’adin kwanaki 10 ga babban bankin kasa ya yi na daina amfani da tsoffin takardun kudi, har yanzu al’umma na janye jikinsu daga karbar tsoffin kudin domin gujewa yin asara.

Wannan ne ya haifar da koma baya a bangaren kasuwanci, musamman yadda ‘yan kasuwar ke kokawa da rashin ciniki.

Haka zalika harkokin kananan kasuwanci irin su awara, kosai, rake, kayan miya a unguwanni, mai shayi da dai sauransu su ma sun samu koma baya saboda basa samun ciniki, sai dai idan kudin da yawa ayi musu tiransifa, ko kuma su hakura da cinikin.

A hannu guda suma mata masu sana’o’i a cikin gida, sun bayyana cewa ‘a wannan tsukun sana’arsu na cikin mutu kokwai, rai kokwai, domin kuwa matsalar na nema ta kassara musu sana’o’i’nsu, don kuwa tun suna bayarwa bashi har ta kai ga wasunsu sun daina abincin da suke siyarwa.’

Su kuwa matan da ke cikin gida cewa sukayi ‘a wasu lokutan ma abincin cin shi suke ba miya, saboda in sunje siyan kayan miya, ba’a karbar tsohon kudi, yayin da wasu kuma su ka ce rashin kudin ne ke sanya su cin gayan abinci, saboda kudinsu yana banki, kuma ba damar cirowa, yayin da wadanda basa iya ajiye kayan abincin ma a gida, sai dai su siya kullum, abincin ma yafi karfinsu, saboda rashin kudin.’

Al’umma dai da yan kasuwa na fatan mahukunta za su duba halin da ake ciki na rashin kudi a hannun jama’a da ma illar da kasuwanci yake fuskanta don samar da mafita kafin lamarin ya gagari Kundila.

Yanzu haka dai masu kananan sana’o’i na kauracewa kasuwancinsu domin gujewa karbar tsoffin takardun kudin da aka sanyawa wa’adin daina amfani da su, yayin da su kuma manyan yan kasuwa ke ci gaba da kasuwancin susai dai rashin kudi a hannun mutane ya haifar da tsayawar kasuwancinsu cak.’

‘Yan kasuwa wadanda har yanzu yan kasuwar ke ci gaba da nuna fargaba kan yadda harkokin kasuwancinsu ya durkushe a yan kwanakin, sakamakon rashin kudi a hannun mutane da kuma matsalar network da ake fuskanta yayin da kwastomomi ke tura kudi ta banki.

A cewar yan kasuwar ;har yanzu tsoffin kudi mutane ke kai musu kuma babu wadatattun kudi a wajen masu cire kudi ta POS.’

Ratoto:Daga wakilanmu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!