Labarai
Babbar kotun daukaka kara ta umarci yan sanda su cafke Abdullahi Abbas tare da bincikarsa
Babbar kotun daukaka kara a jihar Kano, ta umarci kwamishinan ‘yan sandan da ya gudabar bincika tare da kama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abullahi Abbas, bisa zarginsa da zagi hadi da barazanar kisa ga Muhammad Lamido.
Sai dai bayan nadar muryar shugaban jam’iyyar Muhammad Lamido ya yi lokacin da yake cin zarafin sa, Lauyan sa Barister Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi ya shigar da kara a gaban kotun Mai shari’a A.S. Ambode, inda alkalin ya umarci kwamishinan ‘yan sandan da ya yi bincika tare da cafke Abdullahi Abbas.
A zantawarsa da Freedom radio Barister Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi, ya bayyana dalilan da suka sanya wanda yake karewa daukar matakin shari’a.
Latsa nan domin sauraron lauya
Sai dai duk kokarin ji daga bakin Abdullahi Abbas kan wannan lamari hakan mu ya ci tura, amma da zarar ya magantu zaku ji mu da shi.
Mai shari’a A.S. Ambode ya kuma sanya ranar 16 ga wannan watan da muke ciki na Faburairu domin ci gaba da sauraron shir’ar.
You must be logged in to post a comment Login