Addini
Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano
Gidauniyar Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, ta gudanar addu’a ta musamman dangane da cutar Corona Virus , da ta addabi al’ummar duniya baki daya.
Taron addu’ar ya samu halartar dumbin al’ummar Musulmi duk da kiraye -kirayen da masana harkokin kiwon lafiya ke yi , na rage mu’amala a cikin mutane don rage yaduwar cutar, an kuma gudanar da taron ne a rufafen dakin taro na filin wasa na Sani Abachi dake Kofar Mata.
Da yake jawabi a wajen taron addu’ar Shugaban Darikar Kadiriya na Africa, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, ya ce kaucewa tafarkin Ubangiji Allah (SAW) ya sanya yawaitar cututtuka masu addabar mutane ,kasancewar addinin Musulunci yazo da tsarin rayuwa mai inganci wacce da zarar an bi tafarkin ta zata datar da al’umma.
Karin labarai:
Kano : Ma’aikatu 2 za su hada kai don yaki da cutar Coronavirus
Kano: Babu rahoton bullar cutar COVID-19 -Dr, Aminu Tsanyawa
Sheikh Karibullah, ya yi kira ga al’umma da su ji tsoron Allah, tare da yawaita tuba da kula da tsaftar muhali domin kare kansu da kwayar cutar ta Corona.
A wajen taron Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda Dan Amar din Kano Alhaji Umar Shehu Harazimi, ya wakilce shi ya yi kira ga hakiman sa dasu yi duk mai yiwuwa wajen fadakarwa da gangamin wayar da kan jama’ar su don maganin cutar .
Shamsu Dau Abdullahi, wakilinmu da ya halarci taron addu’ar , ya rawaito cewa manyan malamai da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro na daga cikin wanda suka hallarci taron addu’ar da ya gudana a yau Asabar .
You must be logged in to post a comment Login