Kiwon Lafiya
Mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a Katsina
Mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a Katsina
Akalla mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a wasu kananan hukumomin guda biyu na Danmusa da Kankara da ke jihar katsina
Mataimakin gwamna jihar Katsina Mannir Yakubu ne ya bayyana haka a yayin da ya ke kaddamar da aikin riga kafin zazzabin ciwon shawara a makon da ya gabata.
Mataimakin gwamna ya ce kaddamar da riga kafin wani yunkuri ne da gwamnatin su ta dauka domin dakile yaduwar cutar zazzabin ciwon shawara.
Ya ce ana kyautata zaton aikin riga kafin zai kai ga akalla mutane miliyan bakwai, inda yake jaddada cewar zazzabin ciwon shawara zazzabi ne mai yaduwa wanda ake daukarsa ta hanyar cizon wasu nau’ikan sauro da ke cizon mutane.
Mataimakin gwamna wanda babban sakataren ma’aikatar lafiya ya wakilce shi Dr Kabir Mustapha, ya bukaci al’umma da su tabbatar da sun kare kansu da kamuwa da wannan ciwo ta hanyar karbar riga kafin zazzabin ciwon shawara , wanda yake kyauta ne, ake kuma bukatar ‘yan shekaru 9 zuwa 44 ne zasu karbi wannan riga kafin.
Da yake gudanar da jawabinsa a yayin kaddamar da wannan riga kafin, shugaba harkar sadarwa na asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya Musa Rabiu ya tabbatar da bada ta su gudumuwar wajen aiki da gwamnatin jihar ta Katsina don wayar da kan al’umma dangane da matsaloli kiwon lafiya da ke addabar yan jihar.