Labarai
Mutane 40 sun mutu a sabon harin da ‘Yan binding suka kai a Zamfara.
Ana zargin mutane 40 ne suka rasa rayukan su a wani sabon harin da ‘Yan binding suka kai a kauyuka 2 da ke jihar Zamfara.
Awanni 24 ne kenan bayan da gwamnan jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso tsakiya na jihar.
Abdul’aziz Yari, ya kara da cewa Gwamnatin sa ta baiwa hukumomin tsaro umarnin da su bankado ‘yan bindigar don fuskantar hukunci mai tsanani.
Sabon harin dai ya afku ne a yankin Danjibga da sauran yankuna cikin karamar kananan hukumomin Shinkafi da Anka, yayin da ‘yan bindigar suka yi amfani da Babura wajen kai hare-haren.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ta Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar alamarin yana mai cewa bayan mutum 40 da suka rasa rayukan su, kawo yanzu rundunar na cigaba da bincike kan irin asarar da aka tafka.
SP Muhammad Shehu ya kuma sheda cewar nan gaba kadan ne rundunar zata yi taron manema labarai.