Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Harin ‘yan bindiga : Mutane sun rasa rayukan su a Bauchi

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane biyu  sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai yankin Gudum Hausawa da ke garin Bauchi a jiya lahadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ahmad Wakil ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Lawal Jimeta ya bayar da umarnin aikewa da jami’ansu yankin da lamarin ya faru domin fara bincike a kai.

Ahmad Wakil ya bukaci al’ummar yankin su baiwa rundunar hadin kai wajen bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano bata-garin da ake zargi da aikata laifin.

‘Yan bindiga sun sace hakimi a Zamfara

Wasu jami’an yan sanda 3 sun mutu sakamakon harin yan bindiga da ya rutsa da su a jihar Nassarawa

Buhari ya yi tir da harin da aka kai wa ma’aikatan bada agaji a Borno

Gawarwaki biyu dai aka tsinta na wani mutum da wata matashiya bayan da ‘yan bindigar suka shiga garin, kuma har yanzu babu labarin dalilin harin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!