Labarai
Hare-haren ƴan bindiga ya shafi mutane 2,027 a Katsina – Masari
A kalla mutane dubu biyu da ashirin da bakwai ne wadanda hare-haren ‘yan bindiga ya tilastawa barin matsugunarsu, su ka dawo gidajensu a jihar Katsina.
Mutanen dai sun fito ne daga kauyuka hudu dake yankin karamar hukumar Jibiya.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ya ce ,gwamnatin jihar ta Katsina ce dai ta kai wa mutanen dauki don ganin sun dawo muhallansu a jiya Litinin.
Kauyukan da mutanen suka fito sun hada da:Tsamben-Tsauni da Tsamben-Kotumbo da Tsambe-Radi da kuma Tsamben-Zango.
A ranakun Talata da Larabar makon da ya gabata ne dai maharan suka kai harin ta’addancin garuruwan wanda suka tilastawa da yawa daga cikin al’ummar garuruwan yin hijira.
Da yake zantawa da manema labarai, mai garin Tsamben-Tsauni Malam Ibrahim Ali Magarin, ya ce, gwamnatin jihar ta Katsina ce ta kai musu dauki inda suka fara dawowa gidajensu a jiya Litinin.
You must be logged in to post a comment Login