Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu : Matasa na zanga-zanga a Katsina

Published

on

Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Katsina inda suka tare hanyar da ta haɗa garin Jibiya zuwa birnin Katsina sakamakon yadda ƴan bindiga ke ci gaba da kai masu hare-hare.

Sama da mutanen garuruwa goma ne suka haɗu wajen zanga-zangar wadda rahotanni suka ce ta haddasa mutuwar wani matashi wasu da dama kuma suka jikkata a cewar wani ganau da ya shedawa wakilin Freedom Radiyo Yusuf Ibrahim Jargaba a Katsina.

Kakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina SP Isa Gambo, ya tabbatar da zanga-zangar  yana mai cewar suna nan suna ƙoƙarin shawo kan masu al’amarin kuma nan gaba kadan  za su fitar da cikakken bayani a kai.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da al’umma ke yin zanga-zanga a jihar ta Katsina kan matsalar tsaro da ya addabe su.

A ya yin da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin sa za ta tattauna da mutanen da ake zargi da kai hare-hare da satar mutane domin karbar kudin fansa don kawo karshen matsalar tsaro da take addabar jihar.

An dai jiyo daraktan yada labaran gwamnan jihar, Audu Labaran, na shedawa manema labarai cewa  wannan bashi ne karon farko da gwamna Masari ke cewa  zai shiga daji domin tattaunawa da masu kai hare-haren a Katsina

daraktan yada labaran na fadin hakan ne a ya yin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da aka yi a fadar gwamnatin ta Katsina a kwanakin baya.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!