Labarai
Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Niger sun haura 200

Jami’ai a jihar Neja sun tabbatar da cewa, mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a garin Mokwa na jihar sun haura 200.
Kana akwai wasu kusan 500 da ba a gani ba har lokacin fitar da rahoton, yayin da ake ci gaba da yin aikin ceto.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Mokwa, Musa Kimboku, ne tabbatar da hakan a ganawarsada BBC ya na mai cewa an dakatar da aikin ceto saboda hukumomi sun yi imanin cewa watakila babu wanda ya rage da rai.
Ambaliyar wadda aka bayyana cewa ba a ga irinta ba tsawon shekara 60, ta lalata gidaje a unguwannin Tiffin Maza da Hausawa bayan tafka mamakon ruwan sama ranar Larabar makon da ya gabata da daddare.
Tuni dai Hukumomi suka ce za su fara tono gawawwaki da aka binne don bincike, a wani yunkuri na kauce wa yaɗuwar cutuka, kamar yadda Mai garin Mokwa Muhammad Aliyu ya bayyana.
You must be logged in to post a comment Login