Labarai
Mutanen da suka rasu a girgizar ƙasar Afghanistan sun haura 800
Mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Afghanistan ya zarta dari 800, yayain da kusan 3,000 suka jikkata.
Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.0 ta auka wa gabashin ƙasar da tsakar daren ranar Lahadi.
Jami’ai sun ce an samu mafi yawan mace-macen a lardin Kunar.
Inda Jami’a suka yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙaruwar alƙaluman mace-macen, yayin da ƙauyuka da dama suka ruguje.
Iftila’in na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ta Afghanistan ke fama da matsanancin fari, da yankewar agaji abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da mummunar yunwa.
You must be logged in to post a comment Login