Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

UNICEF:Najeriya na matsayi na 11 a kasashen duniya dake samun mace-macen jarirai

Published

on

Asusun kula da kananan yara na majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanya Najeriya a matsayi na 11 cikin kasashen Duniya da ake samun mace-macen jarirai a Duniya.

UNICEF t ace duk da kyautatuwar al’amura da aka fara samu amma har yanzu ana samun jan kafa wajen ci gaban, inda akalla jarirar 29 ke mutuwa a cikin guda dubu daya da ake haifa.

A wata kididdiga da hukumar ta tattara shekarar 2016 zuwa 2017, ta nuna cewa jarirai 37 ne su ke mutuwa daga cikin dubu guda da aka haifa a fadin kasar nan.

Wakilin UNICEF a kasar nan Muhammad Fall ya ce sabon rahoton da suka samu ya nuna cewa jarirai miliyan daya ne suke mutuwa yayin haihuwa a Duniya baki-daya, yayin da miliyan biyu da dubu dari shida ke mutuwa kasa da wata daya da haifarsu.

Ya kuma bayyana yankin kudu da Saharar Afirka a matsayin inda lamarin ya fi kamari, a don haka ya ce akwai daukar matakan gaggawa da su ka dace domin dakile matsalar da hanzari.

Haka zalika Muhammad Fall ya alakanta yawaitar mutuwar jariran da talauci wanda ya sanya mata masu dauke da juna-biyu bas a iya samun taimakon das u ke bukata a kan lokaci yayin haihuwa, baya ga yake-yake da makamantansu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!