Labarai
Mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin ruwan Neja sun karu zuwa 60

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta ce, zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasu sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya afku ya kai zuwa 60.
A baya dai, rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ruwan wanda ke ɗauke da fasinjoji 90 waɗanda ya ɗauka daga mazaɓar Tugan Sule, da ke yankin ƙaramar hukumar Borgu ta jihar, ya yi hatsari.
Bayan aukuwar hatsarin kuma, a ranar litinin ɗin da ta gabata hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, ta bakin shugabanta, Abdullahi Baba Arah, ta tabbatar da samun gawarwakin mutum 29 daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito cewa, an ƙara samun gawarwakin mutane inda adadin ya ƙaru zuwa 60.
You must be logged in to post a comment Login