Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mutum Mutumin Arsenal: Ozil zai cigaba da biyan albashin sa

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil ya nemi a bashi dama don ya cigaba da biyan albashin Jerry Quy, da ke yin shigar mutum mutumin Gunners.

A dai ranar Litinin ne kungiyar ta sanar cewa Jerry wanda shi ne ke shigar mutum mutumin Arsenal tsawon shekara 27, yana daga cikin mutane 55 da kungiyar ta kora daga aiki.

Ozil ya ce “Na yi alkawarin zan cigaba da biyan Jerry Quy kudin albashin sa da Arsenal ke biyan sa domin ya samu damar cigaba da aikin sa da yafi kauna kuma ya dade ya nayi.”

Kungiyar ta Arsenal ta fara rage ma’aikatanta lamarin da ta ce ya zama wajibi, saboda tabarbarewar tattalin arziki da cutar COVID-19 ta hadasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!