Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti

Published

on

Mutumin da ya daure ‘ya’yan sa shekaru 3 a Kano ya rasu a Asibiti

Da safiyar yau ne babban Kwamandan Hukumar yaki da safarar bil Adama ta kasa NAPTIP shiyyar Kano Shehu Umar ya sanar da cewar mutumin da ake zargi   Malam Muhammadu Ojudi dake  garin Rinji a  karamar hukumar Madobi da laifin daure ‘ya ‘yan sa biyu da sarka da kuma sasari ya rasu a yau Juma’a a asibiti  a dai-dai lokacin da ake shirin fara bincikar sa, kan laifin da ya aikata.

Sai dai gabanin rasuwar wanda ake zargi da aikata wannan lamari Muhammadu Ojudi ya bayyana dalilin sa na daukar wannan Mataki na daure yayan nasa biyu.

Amma  dai kwamandan Hukumar shiyyar Kano Shehu Umar yace zasu cigaba da fadada bincike kan alamarin duk da rasuwar wanda ake zargi domin gano musabbabin daukar wannan mataki akan ‘ya’yan nasa.

 

Ana zargin Mutumin da ya daure ‘’yayansa  biyu kan ‘yar taki zaman aure yayin da kuma dansa yake zargin cewar yana shaye shaye, a don haka ya dauki matakin ya sanya su a mari.

Mai haifin yaran yayi ikirarin cewar ‘ya’yan nasa na gagara kasancewar haka ya wajaba ya dauki matakin ya garkame su a cikin daki don su shiga taitayin su.

Malam Muhammad Ujudu  ya rabo da mahaifiyar ‘ya’yan ne tun da jimawa, yayin da kuma yake zaune da kishiyar uwar su

Rahotanin sun bayyana cewar Mallam Muhammad Ujudu  ya daure  ‘yar tasa  a wurin ne take Kashi da fitsari take kuma cin abinci kamar karya, yayin da ake miko mata ta taga.

Shi ma namijin ya shiga matsala irin wannnan ta daure shi da aka yi da sasari sannan sakamakon matsi da ya yi hakan yayi  sanadiyyar rasuwar sa.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!