Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na bada umarnin a harbe duk wanda yayi goyo a Babur – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta bada umarnin harbe duk me baburin da aka samu da goya mutane biyu aka kuma tsayar da shi yaki tsayawa.
Mai Magana da yawun gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle, Zailani Baffa ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radiyo a jihar.
Zailani Baffa ya ce an hana hawa babur daga karfe shida na yamma zuwa wayewar gari.
Sannan ya ce an soke sayar da mai na jarka a fadin jihar tare da hana gidajen mai sayar da mai sai dai a shalkwatar karamar hukuma shima baza’a zubawa mutum sama da na naira dubu goma ba.
Kazalika ya ce duk motar da aka samu da abinci za’a bincike ta, sannan an hana shiga da fitar da shanu a fadin jihar ta Zamfara.
Zailani Baffa ya ce an soke cin kasuwa ta mako-mako da aka saba ci har sai lokacin da gwamnati taga dacewar dawo da ci gaba da cin kasuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!