Connect with us

Labarai

Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 4 a jihar Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da yin garkuwa da mutane 4 a karamar hukumar Sabon Gari dake masarautar Zazzau.

Mai Magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jalige ne ya tabbatar da hakan jiya Juma’a ga manema labarai.

Ya ce mutanan da aka yi garkuwar da su sun fito ne daga unguwar Liman da Zangon Shahu dake karamar hukumar ta Sabon Gari.

Jaligi ya kuma ce mutanan da ‘yan bundigar sukayi garkuwar da su sun hadar da Maza 3 da mace guda 1.

Ya kuma roki al’ummar jihar da su taya rundunar aikin da take na kula da tsaro a jihar musamman wajen sanar mata da duk wasu maboyar bata gari ko ‘yan ta’adda da suka gani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!