Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na matsu na sauka daga mulkin Nijeriya- Shugaba Buhari

Published

on

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya sake nanata cewa ya ‘kagu ya bar karagar mulki.

Shugaba Buhari, ya furta hakan ne yayin da ya ke yin bankwana da jakadiyar Amurika a Nijeriya mai barin gado Mary Beth Leonard, a fadar mulki ta Aso Villa da ke birnin tarraya Abuja.

Haka kuma ya ce, tini ya kammala shirinsa na komawa domin ci gaba da aikin kula da gonarsa wadda ke da dabbobi fiye da dari uku a mahaifarsa da ke garin Daura na jihar Katsina.

 

A baya dai an sha jiyo shugaban na cewa a kullum yana kirgen kwanakin da suka rage masa ya mika mulki a ranar 29 ta watan Mayu mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!