Labarai
Na Sauya Sheka Zuwa SDP ne Don Gina Siyasa Marar Uban Gida-El-Rufa’i

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce sauya jam’iyya zuwa Social Democratic Party (SDP) ya samo asali ne daga bukatar kafa wata sabuwar jam’iyya da ba ta da tasirin Uban Gida da rikice-rikicen cikin gida.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yau Litinin yayin ganawa da manema labarai. Ya ce ya kai ziyara ga Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da kuma haduwa da shugabannin SDP domin tsara dabarun gina jam’iyyar daga matakin jiha zuwa kasa.
Ya Kuma bayyana cewa Kano tana da matukar muhimmanci a siyasar Najeriya saboda yawan masu kada kuri’a. Don haka, bayan shiga SDP, ya ga dole ne ya tuntubi masu ruwa da tsaki a jihar domin inganta tushen jam’iyyar.
Game da dalilin da ya sa ya bar APC, El-Rufai ya ce abubuwan da suka sa aka kafa APC shekaru goma sha biyu da suka wuce sun sauya, harma ya ce yanzu burin su shi ne hada ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban karkashin SDP domin ceto kasar.
A karshe, El-Rufai ya musanta rade-radin cewa yana yin wannan mataki ne saboda an kore shi daga siyasa, yana mai cewa babu wata bukata ta neman mukami da ya rage masa, illa kawai kokarin ganin Najeriya ta samu mafita.
You must be logged in to post a comment Login