Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya sanya na fice daga PDP – Abba Gida-gida

Published

on

Ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019 Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyya zuwa NNPP.

Abba Kabir ya bayyana ficewarsa a jam’iyyar a ranar Lahadi, yayin wani taro da ya shirya a mazaɓarsa ta Ɗiso da ke ƙaramar hukumar Gwale.

Ya ce “Ba za mu ci gaba da jure zaluncin da jam’iyyar PDP take mana ba, sun jima suna wulaƙanta jagoran Kwankwasiyya, duk da halaccin da yayi musu”.

“A wannan filin muka hadu a shekarar 2018 muka ce mun fice daga APC, saboda zaluncin da ake yiwa talakawa, muka koma PDP da sa ran abubuwa za su sauya” a cewarsa.

Labarai masu alaƙa:

A hukumance Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koma jami’iyyar (NNPP

Haryanzu Kwankwaso na nan a PDP-Bashir Sanata

Ya ci gaba da cewa “Mun ɗauka PDP zata ɗauki darasi ta nunawa al’ummar Kano da suka fito suka zaɓeta a 2019 ƙauna, amma sam sai wulakanci da zalunci”.

“Mun yi zaton akwai banbanci tsakanin APC da PDP, mun dauka za a samu adalci da bunƙasar tattalin arziƙi, za a tallafawa mata da inganta harkokin ilimi, amma sam ba a nan manufarsu take ba”

Abban ya ƙara da cewa “Mun gano ƴan jari hujja ne, an daɗe ana zaluntarmu ana wulakanta jagoran Kwankwasiyya, yanzu lokaci ya yi da masoya Kwankwaso suke kira gareshi, garemu da mu bar zama a cikin wannan azzalumai”.

“An yi nazari an tabbatar da cewa abin da jama’ar Kano suke so shi ne abin da zamu runguma, saboda haka bayan nazari mun yarda cewa wannan jam’iyya ta NNPP ita ce wadda zata taimaki talakawa”.

Hoton wajen taron sauya sheƙar Abba Gida-gida

Hoton wajen taron sauya sheƙar Abba Gida-gida

“Duk inda alheri ya ke a nan muke, duk inda amana take a nan muke, bama cikin azzalumai, ba zamu zauna a cikinsu ba, duk wanda baya son ci gaban al’umma muma bama son shi har a bada”

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya muka yi shawara muka amsa kiran al’umma muka bar jam’iyyar zalunci” a cewar Abba Gida-gida.

Har ila yau ya yi kakkausar suka ga ƴan jam’iyyar PDP inda ya kira su da kalmar munafukai, ya kuma yi tir da PDP kan fifita waɗanda ya ce sun shiga Gwamnatin APC an basu muƙamai ta bayan fage a kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!