Kasuwanci
Gwamnatin Kano na shirin samar wa masu yin Gurasa da Takalma matsuguni

Gwamnatin jihar Kano, ta bayyana kudurinta na samar da wuraren zama da rumbunan kasuwanci ga mata masu sana’ar hada gurasa da kuma masu hada takalma a wasu yankuna na cikin birnin Kano domin saukaka musu gudanar da sana’o’insu.
Wannan na zuwa ne yayin da Kwamishinan zuba jari, Kasuwanci da Masana’antu na jihar, Alhaji Shehu Sagagi, ya kai ziyarar gani da ido a yankunan, a unguwannin Jakara da Cediyar ‘Yan Gurasa da ke karamar hukumar Dala da kuma unguwar Kofar Wambai da Chiromawa.
Kwamishinan ya ce wannan yunkuri wani bangare ne na shirin gwamnati na tallafa wa mata da matasa domin kara habaka tattalin arzikin su da inganta rayuwarsu.
Haka kuma, ya duba kasuwar maruna da ke Kofar Wambai domin ganin hanyoyin da za a bunkasa harkokin kasuwanci a yankin tare da samar da sabbin damammaki ga matasa.
Bugu da ƙari Sagagi ya duba wata sharar bola da ke addabar mazauna yankin Kofar Wambai, inda ya bayar da umarni ga hukumomin da abun ya shafa su gaggauta daukar mataki don magance matsalar, musamman a yanayin damina don gujewa ambaliya da yaduwar cututtuka.
You must be logged in to post a comment Login