Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

PHIMA ta bankado dakin shan magani da ake sayar da miyagun kwayoyi a Kano

Published

on

Hukumar lura da cibiyoyin lafiya da asibitoci masu zaman kansu ta Kano PHIMA ta rufe wani dakin shan magani dake unguwar Rafin Dan Nana a yankin karamar hukumar Gwale.

Hukumar ta PHIMA ce ta sanar da hakan, cikin wata sanarwa mai dauke sa hannun daraktan sashen lura da harhada magunguna na hukumar Abdullahi Abubakar.

Sanarwar ta ce, hukumar ta samu rahotonnin sirri, kan yadda matasa ke zuwa dakin shan magani ba bisa ka’ida ba, wanda bincike ya gano cewar matasa na yawan zuwa wurin musamman a lokacin da dare yayi.

Hukumar ta ce, sakamakon binciken da tayi ya gano cewar ana sayar da miyagun kwayoyi, wanda hukumar ta samu nasarar kama katan-katan na miyagun kwayoyi a wurin.

Yanzu haka dai an cafke wadanda ke lura da wannan dakin shan magani baya ga garkame shi da hukumar tayi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!