Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nishadi

Na yi nadamar yin wasu waƙoƙi – Mudassir Kassim

Published

on

Fitaccen mawaƙin Hausar nan Mudassir Kassim ya ce, yayi nadamar yin wasu waƙoƙi a shekarun baya.

A saƙon da ya wallafa ta shafinsa na Facebook ya ce, nan gaba kaɗan zai bayyana waƙoƙin.

Sannan zai bayyana dalilan da ya sa ya yi nadamar yinsu.

Ga abin da ya wallafa.

Mudassir Kassim dai na cikin fitattun mawaƙa da suka yi tashe daga shekaraun 1990 zuwa 2010 wanda kuma har yanzu ana ci gaba da damawa da shi.

Mawaƙin yana cikin sahun farko na mawaƙan fina-finan Hausa.

Daga cikin waƙoƙinsa da suka fi tashe akwai waƙar “Gari Ya Waye…” da waƙoƙin fim ɗin “Zarge” waɗandan suka haɗa da “Ƙwanƙwan…”.

Ya yi waƙoƙi irin su “Rana ta haska baiwa” da “Sakataye…”, waƙar “Ƙauna, don Allah share babu damuwa”, “Jani mai sona jani…”.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!