Kiwon Lafiya
NAFDAC:ta bukaci al’umma da su lura da irin abinda suke ci ko amfani da su
Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta bukaci al’ummar Najeriya da su rika lura sosai da irin abincin da suke ci ko kuma mayukan jiki da suke amfani da su, domin kula da lafiyar su.
Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa akwai nau’ikan abinci ko kuma man shafawa da ke haddasa ciwon koda, ciwon sikari ko kuma cancer da hawan jinni.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar NAFDAC Abubakar Jimoh ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Ilori na jihar Kwara.
A cewar sa ta’ammali da miyagun kwayoyi na kara ta’azzara a Najeriya, don haka akwai bukatar bullo da waasu sabbin matakai da zasu taimaka gaya wajen dakile matsalar.
Yace abin takaici ne ace Najeriya ce kan gaba cikin kasashen da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a duniya, da kaso goma sha biyar, maimakon kaso biyar da aka kayyade tun farko.
Abubakar Jimoh ya kara da cewa kididdigar rahoton da hukumar ta tattara na nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan goma sha biyar ne ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, yayinda miliyan uku daga cikin su kuma suka mayar da miyagun kwayoyi tamkar abincin su.
Babban jami’in hukumar ta NAFDAC ya bayyana cewa wannan matsalar na daga cikin abinda ya ta’azzara matsalar garkuwa da mutane, tashe-tashen hankula, fashi da makami da kuma tukin ganganci a Najeriya.