Labarai
NAHCON: Muna jiran matakin Saudiyya game da aikin Hajjin bana
Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta ce har yanzu tana jiran matakan da gwamnatin kasar Saudiyya ta dauka game da aikin hajjin shekarar 2020, kafin ta yanke nata matakan.
Babban daraktan hukumar ta NAHCON Alhaji Zikrulla Kunle Hassan ne ya bayyana a hakan lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron karawa juna sani da kungiyar masu kula da aikin Hajji da Umara ta Najeriya ta shirya.
Taron ya mayar da hankali ne kan makomar aikin Hajji da Umara bayan annobar Covid19 da ta addabi duniya yanzu.
Babban daraktan a cikin jawabin nasa, ya bayyana wasu kalubale da annobar Covid-19 ka iya haifarwa ko kuma ta haifar game da aikin Hajji a Najeriya, da kuma matakan da ya kamata maniyyata su bi domin gudanar da aikin hajjin bana, yayinda ake fama da zaman kulle a kasashen duniya.
A cewar sa akwai kyaky-kyawan fata hajjin bana zai iya kasancewa duk da fargabar annobar Covid-19 da ta addabi duniya.
Babban daraktan na NAHCON yace kasar Saudiyya ce kadai zata yanke hukunci game da yadda za a gudanar da aikin hajjin bana ko akasin haka a halin yanzu.
“Muna yanke hukuncinmu mu ne bayan mun samu haske kan matakan da kasar Saudiyya ta dauka a kan abinda ya shafi Hajji da Umara”.
Sai dai ya yi karin haske kan matakan da Saudiyyan ta dauka a baya-bayan nan na bude masallatai domin gudanar da ibadu, da kuma yin sassauci a kan dokar kulle a fadin kasar.
You must be logged in to post a comment Login