Addini
NAHCON ta koka bisa rage wa Najeriya yawan kujerun Hajji

Hukumar Jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta bayyana damuwa kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.
NAHCON ta yi gargaɗiin cewa matakin zai hana mutane da dama zuwa aikin Hajjin a shekara mai zuwa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da Yawun Hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce hukumomin Saudiyya sun sanar da NAHCON cewa wuraren kwanan mutum 66,910 kawai aka keɓe wa ƙasar, wani abu da ke nuna adadin maniyyatan da aka ware wa Najeriyar.
Hukumar ta NAHCON ta ce hukumomin Saudiyyar sun ɗauki matakin ne saboda Najeria ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025.
Matakin na Saudiyyar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa , Bola Tinubu ya umarci hukumar NAHCON ta rage kuɗin aikin hajjin 2026.
You must be logged in to post a comment Login