Labarai
NAHCON ta sha alwashin ganin an yi Hajjin badi cikin tsari da kwanciyar hankali

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sha alwashin gudanar da aikin Hajji badi cikin kyakkyawar tsari da kwanciyar hankali ga Alhazai kasar nan.
Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana hakan a taron duba ayyuka da aka gudanar, game da bukatar dukkan jami’ai su tashi tsaye wajen tabbatar da Alhazai sun samu ingantacciyar hidima tun daga Madinah.
Shugaban ya kara da cewa, sauye-sauyen manufofi da fasaha a Saudiyya na bukatar jami’an hukumar su rika sabunta ilimi su akai-akai, yana mai cewa, matsalolin da aka samu a bara ya kamata su zama gyara a bana.
Taron ya tabbatar da kudirin NAHCON na gudanar da hajj ingantacce da tsari da kwanciyar hankali ga Alhazan kasar nan a shekara mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login