Addini
NAHCON ta yabawa jihar Kano kan hukumar jin dadin alhazai – Ganduje
Hukumar kula da ayyukan aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana cewar jihar Kano ce ke da hukumar kula da jindadin alhazai mai kyau daga cikin jihohin kasar.
Babban sakataren hukumar ta NAHCON Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a ya yin da ya kai ziyarar aiki ga gwamnan jihar Abdllahi Umar Ganduje a gidan saukar baki na gwamnati dake Asokoro a babban birnin tarayya Abuja a yau Litinin.
Wannan na kunshe cikin sanarwa da sakataren yada ga gwannan Abba Anwar ya fitar aka rabawa manema labarai cewa babban sakataren ya kai wa gwamnan ziyarar ne a lokacin da ake gudanar da taron majalisar zartarwa ta jiha a can Abujan.
Alhaji Zilkirullah Kunle ya hukumar ta NAHCON ta baiwa gwamnan Ganduje tabbacin yin aiki tare wajen inganta harkokin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano.
Da yake jawabi gwamnan Kano Ganduje jihar Kano tamkar gida ne ga hukumar ta NACON kasancewar ita ce cibiyar kula da alhazai a da tun lokacin da ake hawa dawakai, a don haka gwamnatin Kano ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen yin aiki tare.
You must be logged in to post a comment Login