Labarai
NAHCON zata fara karbar kudin Hajji badi
Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin fara karbar kudin kafin alkalami na aikin Hajjin shekara mai zuwa, Wanda ya kama naira miliyan hudu da dubu dari biyar.
Hakan ya biyo bayan kujeru dubu biyar da da dari Tara da talatin da hudu da NAHCON ta baiwa Jihar Kano a wani bangare na shirye – shiryen fara gudanarda aikin Hajji mai zuwa.
Babban Daraktan hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihar Kano Alhaji Lamin Rabiu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a yayin da yake kaddamar da fara siyarwa da shuwagabannin Alhazai na kananan hukumomin Jihar Kano 44 kujerun aikin Hajji mai zuwa domin su fara karbar kudaden maniyya na wannan shekara.
Lamin Rabiu yace ‘sun dauki matakin fara sayar da kujerun ne sakamakon yadda hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta bada umarni, kuma sun raba adadin kujerun da NAHCON ta basu kimanin dubu biyar da dari tara da talatin da hudu zuwa gida biyu, bangaren sauran Alhazai da kuma bangaren Alhazai masu Adashin gata na Hajj Savings Schame’.
Haka zalika Alhaji Lamin Rabiu Dan Baffa ya gargadi shuwagabannin Alhazai na kananan hukumomi a fadin Jihar Kano dasu gudanarda ayyukansu cikin gaskia da rukwan amana domin duk wanda ya cutarda bakon Allah to yasan makomarsa domin ya sabawa Allah da manzansa
Freedom Radio ta ruwaito cewa manyan daraktocin hukumar da sauran malamai sun gudanarda jawabi mai dauke da nasiha da kuma ratsa zuciya dake nuna irin illar da cin zarafin Alhazai ko cutar dasu ke dashi a Muslinci musamman akan wadanda ake ganin baki ne basu taba zuwa ba.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
You must be logged in to post a comment Login